YaƙinZaune: Finafinai a Matsayin Makaman Yaƙar Tunanin Al’umma (Ƙalubale Ga Hausawa)

Authors

  • Yakubu Aliyu Gobir & Abu-Ubaida Sani Author

Keywords:

Finafinai, Hausawa, Al’ada, Farfaganda, Makisanci

Abstract

Masana da marubuta da dama, sun tabbatar da dangantakar adabi da tunanin al’umma a cikin rubuce-rubucensu mabambanta. Finafinai na ɗaya daga cikin rukunnen adabin zamani da ya samu karɓuwa tare da mamaye zukatan jama’a. Za a iya cewa, fim a duniyar yau, tamkar ruwan dare ne wanda ya karaɗe dukkan nahiyoyi. Lura da haka, bai zama abin mamaki ba, yayin da gwamnatocin ƙasashen da suka bunƙasa ke amfani da masana’antun finafinan da ke ƙarƙashinsu, domin yaɗa saƙonnin da suka shafi manufofi da muradunsu da cigabansu, har ma da farfagandar ruruta ƙarfin iko da suke da shi. A bisa wannan matashiya ne maƙalar ta ƙudiri aniyar bitar tasirin finafinai wajen ɗaukaka matsayin al’umma a idon duniya. Maƙalar ta bibiyi wasu finafinan ƙetare domin bayyana yadda irin waɗannan ƙasashe ke amfani da finafinai wajen ɗaukaka matsayinsu da nuna fasaharsu. A ɓangare ɗaya kuwa, maƙalar ta dubi wasu finafinan Hausa domin duba yadda lamarin yake. A hasashen wannan bincike, sau da dama finafinan Hausa na daƙushe martaba da fikirar Hausawa da ma Nijeriya baki ɗaya, a maimakon ɗaukaka darajarsu da fasaharsu. Ra’in da aka gina takardar a kai shi ne makisanci (Marxism). Maƙalar ta yi amfani da Ra’in Makisancin Fim (Marxism Film Theory) wajen nazartar wasu finafinai da suka haɗa da na Hausa da kuma na ƙetare. Sannan an yi amfani da salon hira a matsayin hanyar samun bayanan da aka gina sakamakon binciken kansu. Binciken ya gano cewa, an bar finafinan Hausa a baya wajen ƙoƙarin bunƙasa al’ada da bayyana ci gaban ƙasar Hausa. Daga ƙarshe takardar ta ba da shawarwari. Ɗaya daga cikinsu shi ne, masu shirya finafinai su yi aiki hannu da hannu tare da masana Hausa domin gano inda za a yi a tufkar hanci.

Downloads

Published

2020-09-20